Labari mai dadi ga dukkan daliban Nigeria! Gwamnatin Tarayya ta karkashin Shugaba Tinubu ta bude sabon tallafin karatu wanda ake kira NELFUND Student Loan. Wannan ba kamar sauran loan din bane, wannan tallafi ne na musamman don dalibai su biya kudin makaranta da kuma samun kudin cefane.
Mutane da yawa suna tunanin cewa sai masu godfather ne ke samun wannan loan din, amma gaskiya ba haka bane. Duk dalibin da yake jami'a, polytechnic ko College of Education na gwamnati ya cancanta.
A cikin wannan labarin zan nuna muku yadda zaku cike wannan loan din da waya kawai ba tare da kun je wani cafe ba.
WANE NE YA CANCANTA?
1. Dole ka kasance dan Nigeria
2. Dole ka kasance dalibi a jami'a ta gwamnati, Federal Polytechnic ko College of Education
3. Dole ka kasance kana da admission letter
4. Dole ka kasance kana da NIN (National Identification Number)
5. Dole ka kasance kana da BVN
6. Dole ka kasance kana da student ID card
NAWA NE AKE BAYARWA?
Gwamnati tana bada har N500,000 ga kowane dalibi. Wannan kudin ya kasu gida biyu: Wani bangare zai je kai tsaye zuwa makarantar ka don biyan tuition fee, wani bangaren kuma zai shigo account dinka kai tsaye don cefane, littafai da sauran abubuwa.
Wannan ba bashi bane da za ka biya nan take. Za ka fara biya ne bayan ka kammala karatu da shekara biyu kuma ka samu aiki. Kuma babu ruwa (interest) mai yawa kamar na banki.
YADDA ZAKA CIKE DA WAYA:
Mataki na 1: Shiga website din su na gaskiya wanda shine nelf.gov.ng. Ka lura, kada ka shiga wani link na karya da ake yadawa a WhatsApp.
Mataki na 2: Ka danna Apply Now. Za su bukaci ka bude account da email dinka.
Mataki na 3: Ka cike bayananka kamar sunan ka, makaranta, course, level, da kuma NIN da BVN dinka.
Mataki na 4: Ka saka account number dinka na banki ko Opay inda za su tura maka kudin cefane.
Mataki na 5: Ka saka admission letter dinka da kuma student ID card dinka.
Mataki na 6: Ka danna Submit.
Bayan ka cike, za su duba bayananka kuma idan komai yayi daidai, za su turo maka SMS a cikin mako 2 zuwa 3.
GARGADI MAI MUHIMMANCI:
Kada ka biya kowa kudi don ya cike maka. Cikewa kyauta ne gaba daya. Kuma kada ka bayar da NIN da BVN dinka ga kowa a WhatsApp. Mutane da yawa sun yi scamming da sunan NELFUND.
Idan kana da matsala wurin cikewa, ka je Students Affairs na makarantar ka za su taimaka maka.
Wannan dama ce ga dalibai don kada su daina karatu saboda rashin kudi. Ka yi amfani da ita yau.
Allah ya sa mu dace.
You must be logged in to post a comment.