Yanzu haka kowa yana neman hanyar samun kudi a internet, amma mafi yawan hanyoyin da ake tallatawa a WhatsApp da Facebook karya ne ko kuma sai ka kawo mutane sannan za a biya ka. A matsayina na dalibi da nake amfani da waya kawai, na gwada hanyoyi da yawa kuma na gano guda 4 da suke aiki da gaske ba tare da ka saka ko sisi ba.
A cikin wannan labarin zan bayyana muku su dalla-dalla.
HANYA TA FARKO - LODPOST.COM (Rubuta Labari):
Wannan ita ce hanyar da nake samun kudi yanzu. Lodpost dandali ne da zaka rubuta labari da waya kawai, idan mutane suka karanta za su biya ka.
Yadda yake aiki: Ka je lodpost.com ka bude account kyauta. Sannan ka danna Write Article. Ka rubuta labari mai amfani kamar "Yadda ake samun MTN data" ko "Yadda ake cike FG loan" ko "Yadda ake duba JAMB result". Idan mutum 1000 suka karanta labarin ka, zaka samu $1 zuwa $3. Abin mamaki shine zaka iya cire kudi daga $1 kacal. Ba sai ka tara $50 ba. Kuma ba sai ka yi referral ba. Sirrin samun views shine ka rubuta abinda mutane ke nema a Google kuma ka yada link din ka a WhatsApp Status da Facebook Groups. Ni na fara da $0.25 kyauta da suka bani, yanzu ina kokarin tara $10 na farko.
HANYA TA BIYU - PREMISE APP (Amsa Tambayoyi Da Daukar Hoto):
Premise app ne wanda zaka sauke a Playstore. Wannan app din yana baka karamin aiki kamar su je kasuwa ka dauki hoton farashin shinkafa, ko su tambaye ka hanyar da kake bi zuwa makaranta. Kowanne aiki suna biyan ka $0.10 zuwa $0.50. Idan ka hada aiki 10 a rana zaka samu $2 wanda yayi kusan N3000. Abin yana aiki a Ibadan, Lagos, Abuja da Kano. Suna biyan ta PayPal ko Mobile Money.
HANYA TA UKU - SPROUTGIGS.COM (Karamin Aiki Na Online):
A Sproutgigs akwai kananan ayyuka da ake kira micro jobs. Misali wani zai ce maka ka yi masa follow a Instagram zai biya ka N100, ko ka yi subscribe a YouTube channel dinsa zai biya ka N150, ko ka sauke app. Aikin bai wuce minti 5 ba. Idan ka yi aiki 20 a rana zaka samu N2000 zuwa N3000. Da waya kawai zaka iya yin komai.
HANYA TA HUƊU - TALLA KAYAN WANI (Affiliate Marketing):
Wannan ma ba sai ka da kayan ba. Ka je Jumia Affiliate ko Expertnaire. Ka dauki link na wani kaya kamar waya ko takalmi, ka yada a WhatsApp Status dinka. Duk wanda ya saya ta link dinka, zaka samu kudi. Misali idan waya ta N100,000 ce kuma commission dinta 5% ne, zaka samu N5000 a sayarwa daya.
SHAWARA TA KARSHE:
Kada ka zuba lokaci a wajen apps da ke cewa suna baka N50,000 a rana ba tare da aiki ba. Duk karya ne. Fara da Lodpost da Premise saboda ba sa bukatar jari. Idan ka dage na sati 2, zaka ga canji. Ni na fara da waya kawai, ba tare da computer ba, kuma yanzu ina samun abinda ya ishe ni na data da cefane.
Ka fara yau, kada ka jira gobe. Allah ya sa mu dace.
You must be logged in to post a comment.