Amman xuciyata ba abun tilastawa bane
Shekara biyu kenan da auren mijina mutumne Mai kyau Yana kawo abinci Yana biyan bukata Amman kalaman soyayya Babu kulawa ta xuciya Babu duk rana Yana waya Yana kasuwanci nikuma Ina xaune ni kadai Ina kallonshi
Akwai saurayina da sunanshi Abdul munyi soyayya har shekara uku mun rabu ba don mun Daina son junabane mun rabune saboda Yan talaka a lokacin iyayena suka hana nayi kuka Mai yawa a lokacin Amman Babu yadda na iya
Yau bayan shekara biyu da rabuwa sai na ganshi a kasuwa ina sayan kayan miya naji Wani yakira sunana ahankali hauwa
Najuya saiga Abdul ya girma yayai kyau ya canja ya Sanya kaya masu kyau yace haryanxu kinada kyau kamarda idanunki haryanxu haka suke
Alaokacin xuciyata tabuga da karfi kaman xata fito duk soyayyar Dana binne tsawan shekara biyu ta dawo a minti Daya
Yabani takarda da numbernsa aciki yace idan ina neman abokin magana ki kiarani
Yanxu darene karfe11 na dare mijina Yana bacci a gefena Yana munshari nikuma Ina xaune cikin duhu Ina kallon number din Abdul awayata hasken wayan shike haska fuskata
Hannuna na rawa shin inkira shi? Idan na kirashi naci amanar mijina xan xama maci amana idan ban kirashiba xanci amanar xuciyata xancigaba da rayuwane cikin bakin ciki har karshen rayuwata
Meya kamata mace tayi a irin wannan halin shin soyayya ta gaskiya tana mutuwa ko kuwa tana vaccine kawai tana jiran lokaci .
KASHI NA BIYU ZAIZO GOBE DA DARE IDAN KUNA SONJI KUYI COMMENT DA SHARE.
You must be logged in to post a comment.