Taba daya ce ta kashe abokina.

Sunana Aliyu.na girma tare da Sule.Mu biyu ne kamar dan uwa.

A 2023,Wani babban dan uwansa,ya kawo mana abin jin dadi yace, taba daya kawai zakuji dadin rayuwa.

Naki.sule yace Aliyu kayi gwaji rayuwa guda dayace.

Na yarda.taba daya ta zama biyu.biyu ta zama kwalba.kwalba ta zama ko wace rana.

Da farko, muna dariya. muna jin mun fi kowa karfi. muna barin sallah.muna barin aiki.iyayen mu sun fara kuka.

Wata rana sule bai tashi ba.yayi yawa. ance overdose.an binne shi a rana daya.

Ni na tsira. amma ba nine na farko ba.Na daina zuwa makaranta.Na daina girmama kaina.Na zama abin tsoro a gida.

**Darasi**

Abin da na gane shine:**shaye_shaye baya kawo farin ciki.yana aro maka dakika 5 na dariya,sai ya dauko maka shekaru 5 na nadama.**

Idan kana karanta wannan kuma kana cikin wannan hali,kasan gaskiya:**baka makare ba.**

Akwai mutanen da zasu taimake ka.ka fara da fada ma wani abinda ke damunka.ka ce, "Na gaji."

Ni na fara haka yau watanni 6 ban taba ba.Ba sauki bane, amma ina raye.

**Kira.**

Idan wannan labarin ya taba ka,share wa abokin ka wanda ke cikin wannan hali.Wata kila kaine dalilin da zai dakata yau.

 

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author